Kadan daga cikin littafin:-
Gudu,gudu sauri
sauri,haka take tfya tanason ta isko dillaliya, dakyar tasamu tacimmata hartasha kwana tana sassarfa,yyinda dillaliya taja tsoki,tareda cewa a haka xaki iya yin aiki a gdan minister nifa ina shakkar ma nabiya kudina natafi daka aki daukarki aikin,gaban jiddah ne ya fadi tareda fadin zan iya mana dillaliya kitaimakamani wlh bazan baki kunya ba,batareda dillaliya takara magana ba ta tare musu mota sai tasha inda suka shiga mota direct sai birnin tarayya abuja,tunda suka shigo abuja gaban jidda ke faduwa,tanata jero addo'oi domin samun nasarar abunda taxo nema,batareda da bata lokaciba suka doshi maitama gidaje ne na alfarma suke giftawa yayinda dillaliya tasaki baki da hanci tana kallo gidajen nan tsararru dasuke wucewa,sabanin jidda dakanta ke kasa tana sake-sake cikin ranta,dillaliya ce ta tabota tana mamakin yanda jidda bata kalle-kalle kamar sauran masu aekin data saba kawowa,tace wai ke kin wani dukar dakai bakya kallon gidajen damuketa wucewa nifa har nama tsorata kada nakoma hanne tatsareni don wlh bazan iya fita daga anguwar nan ba bare dawowa da wani,jidda tayi murmuahin karfin hali tace haba dillaliya nan wurin ne zaki kasa fita? ,harara ta watsamata kafin tace sannu yar birni naga ke kinsaba zuwa ae yarinya sai iyayin tsiya ke komai kinsani kidaiyi ahankali kada wurin iyayenki aki daukarki aikin,jiddah tace insha Allah hakan bazai faruba,dillaliya dai bata amsaba tacigaba daba ido hakkinsa har suka iso katafarin gate din inda sojoji ke zagaye da gidan yayinda dillaliya takara tsorata jidda kuwa hankalinta kwance tana addo'in samun nasara,batareda bata lokaci ba motarsu tayi parking cikin makekiyar rumfar gdan wanda dama motar gdan ce akaje daukosu da ita.suna fitowa sojoji biyu sukayi jagorarsu har zuwa main kofar palon gdan.
Da sallama suka shiga cikin palon fadar yanda palon ya tsaru bata lokacine saboda palo ne wanda yasha kayan alatu yyin da komar nacikinsa ash&black ne.Hajiya Amina ce ta amsa daukeda murmushi a fuskanta tabasu izinin zaunawa tareda bada umarnin kawomasu ruwa,nan fa kallo yadawo sabo wurin dillaliya bayan sha ruwa da lemu ne,dillaliya tayi jawabin yar aikin da aka umurceta takawo tundaga kano,hjy amina tayi gyaran murya tace dafatan dae ta danyi boko don banason jahila kinsani nafadamiki?dillaliya tce kwarai kuwa ranki ya dde tayi boko harda arabi ma,hjya amina tamaida kallonta ga jidda tace ina kika tsaya a skul din,jidda tyi kasa dakai cike da girmamawa tace S.S.1 hjya amina tayi murmushi tace to shikenan zakayima yata zainab aiki tareda kulada ita yanzu tana jarabawar karshe secondry intagama kuma zamu turata india takaranci likita in aikinki yana kyau tareda ke xakutafi domin jigabada kulamun da ita,don sam bata iya wahala ba sai fa karatu takarashe maganar da daria,tajuya taciro dubu dari taba dillaliya tareda fadin Allah y kiyaye hanya,saboda tsabar rudu dillaliya mancewa ma tayi dawata jidda saboda yawan kudinda aka bata har tafita
Post a Comment