Kadan daga ciki:-*Kwance* take akan kujera tayi tagumi da hannun ta tayi nisa a tunani, abin duniya ya ishe ta, Jin an tab'a tane yasa tayi firgigit ta dawo hayacin ta, d'agowa tayi sai taga mijinta ne, murmushi ya sakar mata tare da zama kusa da ita,Ya rik'e hannun ta yace"kyakyawar fuskar ki ya kanyi Muni a duk lokacin da kike cikin damuwa, Wanda damuwar ki yake jefa Ni cikin matsala ko Zaki iya fad'a min yanzu meke damun ki my wife?" Wasu hawaye ne suka zubo mata Nan ta rushe dakuka,cikin rud'ewa yace"Subhanallah please kiyi shiru ki fad'a min mene ne?"
Cikin kuka tace"kasan matsala na meyasa zaka damu da tambaya na, ka fad'a min meyasa bazan Damu ba?" Sauke ajiyar zuciya yayi yace"wifey bana son kina saka damuwa a ranki har ciwo ya Kama min ke,Dan Allah kiyi hak'uri ki kwantar da hankalin ki"
Cikin damuwa tace" sweety kana ganin zan bar damuwa ne, shekaru goma Sha biyu da yin auren mu amma ko b'arin ciki ban tab'a yi ba, meyasa bazan Damu ba, wallahi Ina son haihuwa"ta k'ara fashewa da kuka,
A hankali ya fara Mata nasiha cike da k'aunar ta, har jikinta yayi sanyi, sannan ya samu ta daina kukan, daga nan ta tashi ta had'a Mai dinner,
Washegari da safe
Kasancewar weekend ne, yau tana ta aiki sai ta zauna a parlour Dan ta huta, t.v ta kunna ta fara kallon news can taga ana nuno wani jariri cikin kwali sabuwar haihuwa, mahaifiyar ta Yar da shi bayan ta haifa,haka mutane suka dinga magana akai yanda zamani ya lalace,sai mace tayi cikin shege ta yar da abin da ta haifa,
Ji tayi an rungume ta, tace"yauwa sweety zo kaga meke faruwa" zama yayi kusa da ita Yana kallon news d'in,can ya tashi ya kashe t.v yace"irin wannan abin Sam bai dace kina kallo ba, Dan wannan rashin imani ne mutum ya haihu ya jefar da abin daya haifa"
Tace"gaskiya Babu imani Kam Allah ya Kare mu da aikata zunubi,yanzu mene ne laifin yaran da za'a jefar dasu,wasu na nema wasu na zubarwa"
Yace"Allah ya ganar dasu gaskiya dai"
Tace"Ameen"
Post a Comment