Kadan da cikin littafin :
Tafe nake a cikin wata kasuwar fruits(kayan marmari),nazo wuce wata rumfa,mai dauke da kayan marmari kala
kala, wata kyakkyawar yarinya na hango a ciki, sanye take da wasu kodaddun atamfa riga da skirt,yarinyar ba zata
wuce shekaru sha shidda ba, sai tsalle take tana fadin, kuzo ku siya, namu sunfi zaki, tana maganar fuskar ta dauke da
murmushi,
kumatun ta sun lotsa, mutane dayawa suka tsaya a wurin suna kallon ta,kwanin sha'awa, gata kyakkyawa, ta
dauko lemu,ta dauko alaba da sauran fruits din, tana fadi musu anfanin su,dan kawai su siya.Wani mutuni na gani ya kira ta ciki, yarinyar na murmushin mai kara mata kyau, tace ya habu har zamu tashi ne, naga
akwai sauran jama'a a kasuwar, mu dan kara jira kaji, ya habu ya kalle ta yace NI'IMATU, ke bakya gajiya ne , tun
safe kike tsalle tsallen nan, niimatu ta dara, ta kai wa ya habu naushi a hannu, ni ban gaji ba Allah, mudan kara jimawa
kaji, ya habu yayi dariya, ke kam da namiji ce , da anyi jarumi.
Marubuciya:Agra
Category: Love & Romance
Post a Comment