Kadan daga ciki:-A hankali ta tsallako tatitin kai tsaye kuma ta shige dogon layin dake gabanta,ta dubi tsahon layin duk da yawan al'ummar da yake da shi a dade yake babu kowa tankar anyi shara,hakan baya rasa nasaba da irin ranar da ake kodawa kamar mutum yaa dora hannu akansa yace wayyo Allah sannu a hankali take ci gaba da tafiya tamkar mai tausayin qasa,a zahirance idan ka ganta sai kayi tsammanin ranar bata dameta ba saboda yanayin yadda take tafiya,saidai sam tana daga cikin wadanda rabar ma tafi gallaba,don har Allah Allah take taga ta isa gidansu,saboda leshin dake jikinta dinkin riga da skert da kuma dogon hijabinta mai hannu dake qara mata zafi wanda ya zamo too match ne da kaya jaka da 'yar jakar swagger dake maqale a kafadarta babu wata doguwar tafiya ta iso qofar gidan nasu wanda ke rukunin gidajen marasa wadata,duk da ginin bulo da bulo ne saidai bai samu arziqin fulasta ba bare a kai ga fenti,ta cire jakar kafadarta tana shirin shiga soron gidan idanunta ya sauka kan hauwa wadda ta cakare cikin kwalliyar atamfa,wani matashin saurayi ke fiskantarta wadda yanayin tsaiwar tasu kawai zai fahimtar da kai zance suke,dauke kanta tayi tamkar bata gansu ba don wannan dabi'a ta hauwan bama ita ba duka yaran gidan na bata haushi ta tsakiyarsu ta raba zata wuce kasancewar babu wata hanya sai ita taji saurayin na fadin‘’barka da dawowa antyn mu‘’
‘’yauwa sannunku‘’ta amsa masa ba yabo ba fallasa tare da shigewa cikin gidan hauwa dake binta da harara kamar qwayar idonta zai fado ta ja wani matsiyacin tsaki
''gaskiya haruna kana bada ni wallahi,wai kai me yasa kullum baka da,burin da ya wuce ka yarfani a gun wannan matar ne,me ma kake nufi ne ni fa ban gane ba''
''yanzu laifi ne kulu don na gaisheda yayarki,kuma fa kin sani tana da kirki wlh,uwa uba ilimi da nutsuwa'' cike da masifa hauwa ta qwalalo ido ''iyeee,to ko zaka koma gurinta ne haruna,a gabana zaka dinga yaba wata uwar mata da ta shekare gaban iyaye aka rasa mai dauka?''
Author:Safiyya Abdullahi Musa huguma
Category: Love & Fiction
إرسال تعليق