Kadan daga ciki:- daga bakin alkalin wanda yasunkuyar dakansa yana rubuce-rubuce.Lauyoyi dasauran ma,'aikata wadanda suke da alhakin zama akotun sbda sauraron shari'ah, kowanne yana xaune a mazauninsa daya dace dashi,haka yan kallo da iyayen yarinyar da ake gudanar da shari'ar a kanta al'amarin yan ba kowa tausayi shiyasa indai mutum yakalli fuskokin kaso tara cikin
goma na mahalarta kotun sai kaga kowa cikin matsananciyar damuwa musamman wadanda abin yashafa, iyayenta da yan uwanta knan.
Mai shari'ah usman muhammad yadaga kansa a hankali yadubi wacce ake ka ra tana tsaye inda ake tsaida wadanda ake tuhuma hannayenta biyu sanye da ankwa.
Bakar rigace a jikinta da bakin hijjabi sanye akanta, ba dankwali idanuwanta sunyi wani irin ja saboda tsabar kuka, ba ta son dago kai tadubi kowa saboda tsanar kanta datayi don haka ma da alkalin yakira sunanta bata dago kanta ba ta dai amsa cikin dashashiyar murya wadda da kyar ake iya jin abinda ake fada. Alkalin yakuma cewa "Fatima Musa" Ta amsa "Na'am" "Ke kika kashe doctr Abubakar saddik wanda akafi sani da doctr khalifa??? Fatima tayshiru alkali yana maimaita tambayar har sau uku Batayi magan ba, yadda kasan kotun ba kowa saboda tsabar
shiru, koda fatima da mai shari'a yake kallo ana sauraron abinda fatin xa tace amma taja bakinta tayi shiru kamar dam
chan yadda Llah yahalicce ta batada bakin magana.
Mai shari,'a Muhammad Bamaina yana magana cikin yanayi na
tausasa harshe yace "Fatima kotu tana tuhumarki da laifin kashe mijinki Dr. Khalifa kamar yadda ka kamaki da gawarsashiyasa muke son ki bayyanawa kotu gasjiyar al'amari da bakinki tunda ke ba bebiya bace kuma ba kurma bace kina jin abinda muka fada kuma kina iya magana.idan ke kika kashe shi kifadawa kotun sannan kifadi dalilin dayasa kika kashe shi, idan ba ke bce ba to kidanyi magana kiyi bayani. Fatima tadago kanta a karo nafarko tadubi duk jama'ar kotun suka hada ido da mahaifiyarta wadda tazuba tagumi dukda nisan dake tsakaninsu da Fati, Fati ta san kuka take wiwi tana girgiza kai, Fati tadubi mai shari'a sai kawai taj kanta yana juyawa kafafunta suka shiga rawa, hakan yasa suka gaza cigaba da daukar gangar jikinta tazube a gun, nan take mai shari'a Usman M Baina yadaga shari'a zuwa uku ga watan gobe idan Allah ya kaimu.Kotu tarude da hayaniya, koke koken iyayan fati da yan uwanta ya cika kotun ga uar uwarsu a matsananciyar hali amma ba yadda xa ayi su taimaketa, sunaji suna gani wasu yan sanda mata suka daga fati aka fice da ita da gaggawa sbda numfashinta ne yake sama saa kamar zai dauke.
إرسال تعليق